DOWEN COLLEGE LAGOS DEPARTMENT OF LANGUAGES SUBJECT: BAKAKE DA WASULAN HAUSA CLASS: JS2 TEACHER: MRS OGUNDAMOWO E-MAIL ADDRESS: flodan160@yahoo.com SHUGABANCI Ma’anar shugabanci Shugabanci shine daukar nauyi jama’a da yake shugabanta kamar abubuwa rayuwa na yau da kullum: Lafiya,Ilimi,Hanyoyi Wuta d.s IRE-IREN SHUGABANCI 1. Zaman gida 2. Zaman gandu 3. Shugabanci a tsarin mulki i. Dagaci ko magaji ii. Hakimi iii. Sarki 4. 5. Shugabanci fuskar ilimi Shugabanci a fukar Aiki/Sanar. ZAMAN GIDA A wannan tsari mai gida ko Uba shine shugaban gidansa. Matansa,ya’yasa ,yaran gida masu yin masa hidimomi suna karkashinsa a matsayin mabiya. Nauyi ciyarwa da wurin kwanciya ,tuffafi duk ya rataya a yuwar mai gida. Shi ne zai shirya aikin da kowanne su za su yi, ya kuma tabbatar da su yi aiki. Duk wanni abu da ake buka ta a gida shi ake tambaya, sai ya bada izini a ke yin wannan abu a gida. Haka kuma kare lafiyar mutane gida duk ya rataya a yuwarsa. ZAMAN GANDU (BABBAN GIDA) Wannan shine tsari zaman na Bahaushe na asali. A nan ana zaune ne a babban gida tare da ma gidanta fiye da goma. Kowane da yankinsa a gida, in da yake da rukunnin iyalinsa a karkeshi shugabancin (Uban-Gandu) Wannan tsari gandun shugaba daya tal duk abinda ya ce ya zauna. Idan ya yanka bata tashi. Wannan shine dattijjo mafi tsufa a gidan mafi shekaru . wannan tsohon zai kasance da nasa rukunni tare da iyalinsa, a irin wannan gandun akan sami mutane tamanin zuwa dari. Shugaban gandun shi ke kulla da hadin kan jama’ar gandun ,raba aikin a gidan , hakokin aure idan yara sun kai munzulin aure ko sun so , ya kula da rigingimu da kan tashi cikin gandun ya zama alkali, ya yi sharia. Idan ya yanka hukunci ya zaunu. Duka gandun na bin umurninsa.a irin wannan zaman, za ka samu daga kakanni, sai ‘ya’ya da jikoki, wato duk zuriya daya ce babu bare. Wannan zaman yan’uwantaka da kara kulla zumunci da taimakon ‘yan’uwa da hada kai. Lokacin noma sai an yin a gandu kafin a bi gonakin sauran yan’uwa su nome. SHUGABANCIN TSARIN MULKI A. UNGUWA Gidaje suka hadu suka yi unguwa. A kan zabi shugaba guda wato “Mai-unguwa”ya dauki shugabanci sauran’iyayen-gandu da iyalinsu. Galabi, Dagaci ko Magaji yak e zabar Maiunguwa ta hanyar ganawa da sauran jama’ar unguwar wadanda da suke da amincewa da mutumin da za a ba wannan shugabanci. A tsarin mulki dukan ayyukan da hukuma ke so tayi sai an bi wurin mai unguwa, shi ke yin sulhu da shirya jama’a idan rigima ta taso. . miisali na gona, aure ko fada ko sata da dai makamantansu. Ida aka sami rasin yarjejeniya sai a gabatar da shi ga Dagaci . Duk abinda hukuma za ta yi sai sun nemi goynbayansa. B. DAGACI KO MAGAJI A kauye akan sami unguwanni dayawa da gidaje dayawa. Akan zabe shugaban wanda zai lura da kauyen . sarki shi ke ikon nada Dagaci ko magaji. Dagaci shi zai dauki nauyin wannan kauyen. Ta wurinsa ne talakawa zasu gabatar bukatun su zuwa hukuma. Dagaci yana dauka nauyi taimakawa Mai’uguwaninsa. Kokarin Dagaci kullum shi ne ya kyautata rayuwar jama’arsa. C. HAKIMI Hakimi shi ne shugaban gari ko kasa wanda kauyukan Dagaci suna karkashinsa. Sarki shi yake nada Hakimi domin ya lura da mutanensa. Hakimi shi ya ke kula da kauyukan da suke cikin yankin kasarsa. Duk abinda hukuma take bukatar jama’a su yi, shi ne zai tara Dagaci da Maiuguwanni ya ba su umurni, hakimi a matsayin sa na shugaba shi ke kwantar da rigima ko tarzoma da tashi a kasarsa. D. SARKI Wannan shine shugaban Al’umma duka a tsarin mulki. Duk Hakimai, Dagaci, Maiunguwnni da Talakawa suna karkashisa ne a matsayi mabiya. Sarki shi ke jagorancin jama’ar sa a kan kowanne abu da ya shafi rayuwa. Sarki shine Baban kowa. Don haka ake ce dasu “ iyayen jama’a AIKIN GIDA LITTAFI:- Fahimtar Hausa Shafi na 43. Tambaya: Yi bayani a kan wadannan a sarauta Hausawa i. Turaki ii. Yerime iii. Waziri iv Madaki Send your answers to the above e-mail address.
© Copyright 2024 Paperzz