page 33.indd

AMINIYA
Juma’a,12 ga Disamba, 2014
[
Adabi
Adabi
[
33
Tare da
Bashir Yahuza Malumfashi
byahuza03@yahoo.com
(08098157899)
Waqe: Allah Ka ba
mu zaman lafiya
Babu shakka al’amura sun kai intaha, zaman lafiya ya qaura daga Najeriya, musamman ma a yankunan Arewa.
Kullum rana ta lillahi sai an samu labarin tashin hankali, sai an samu labarin mutuwar al’umma da asarar dukiya.
Kamar yadda aka sani, babu wani abu da zai yi tasiri a rayuwa, idan babu zaman lafiya. Al’umma suna cikin
tsoro da fargaba, wasu sun zama ’yan gudun hijira a cikin qasarsu; wasu kuwa sun ma gudu sun bar qasar tasu
ta haihuwa. Babu abin da mutane ke buqata sai zaman lafiya, wanda shi ne abu mafi alheri a rayuwa. domin
ganin an samu zaman lafiya, Dokta Tilde ya xauki alqalaminsa ya kwarara baituka casa’in da tara, wato xari xaya
ba xaya, kamar haka:
Daga Dokta Aliyu U. Tilde
Su je makaranta su qona ta kurmus
Da yara cikinta ga baki xaya.
Ta’ala qadiri Ka ban lafiya
In rera waqen zaman lafiya.
Su ce musu arna da Kalmar Shahada
A baki, su fille su ba yafiya.
Ka ba ni hazaqa har da fasaha
Gurin rera waqar zaman lafiya.
Boko Haramunga sun mana illa
Sun ci amanar zaman lafiya.
Tsira aminci su tabbata gun
Muhammadu manzon zaman lafiya.
Sun watse birni kaza har da qauye
Kowa ta kai nai yake tafiya.
Ba shi kaxai ba har da sahabbai
Da aluh da matansa baki xaya.
Iyali su watse da dangi hakan nan
Kowa a firgice sai tafiya.
Ya bar wasiyya ga umma tasa
Su zanka shiri don zaman lafiya.
Da muggan xiya cikin namu soja
Ba su da niyyar zaman lafiya.
Ya zo da saqo na jalla gare mu
Islam nufinsa zaman lafiya.
A qauye birane misalinsu Baga
Sun yi ta gilla ga baki xaya.
Jigo biyar ne inji Muhamman
Biyo ni ka ji su ga baki xaya.
Sun kashe yara, sun qona mata
Sun kauda daxin zaman lafiya.
Farkonsu Kalmar Shahada ka gane
Biyayya ga Allah zaman lafiya.
Ta’ala mashiryi ga ni gare Ka
Ina zanka roqon zaman lafiya.
Yarda da saqon Muhammadu shi ma
Ya na kai ga turbar zaman lafiya.
Gare ni da ’ya’ya da mata dukkanmu
Da dangi abokai ga baki xaya.
Na biyyunsu Sallah na khamsu biyar ne
Da ba su yuwa sai akwai lafiya.
Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu
Haxa mu zumuncin zaman lafiya.
Ga Ramalana mu zan azuminsa
Kaza ba da Zakka zaman lafiya.
Daxe mu fahimta ta juna mu gane
Cikin arziki ba kamar lafiya.
Cikonnasu Hajji ka je in da hali
Guzuri da hanyarka mai lafiya.
Fitinnu na baya kaza na zamanu
Ka kare mu Jalla mu zam lafiya.
Sahabi ya ce ya Rasulu gaya mun
Zan sam sawaba zaman lafiya?
Mu rungumi ilmu na dini da dunya
Ci gaban rizqu don zaman lafiya.
In na riqe su biyar babu qari?
Manzo ya ce har ka zam lafiya.
Daxe mu da tsoronKa ya Jalla Sarki
Domin Muhamman mijin Mariya.
A gobe qiyama a saka a Jannah
Nan ne tiqewar zaman lafiya.
Ba mu kaxai ba har da Boko Haramun
Yaranmu shirye su baki xaya.
Ta yaya Musulmi a yau sunka bauxe
Wa horo na manzon zaman lafiya?
Qanne da yayye cikinsu gaba xai
Maido su hanyar zaman lafiya.
Su kafirta bayi da Kalmar Shahada
Suna rushe saqon zaman lafiya.
Ka yafe su laifinsu komai yawansa
Bayinka ne Rabbu mai lafiya.
Wasunsu gama har makamai gare su
Gilla suke ba zaman lafiya.
Idan Ka tsane su Allah Gafuru
Waye gare su ko a nan duniya?
A Yerwa da Bama da Baga da Gwoza
Banki, Chibok ba zaman lafiya.
Ka nunan da raina ina sintiri
Da nono a Yerwa zaman lafiya.
Sukan harbe mata da yara da tsofi
Samari su sace su baki xaya.
In je ni Bama in miqa caffa
Gidan Mbusube Baba mai gaskiya.
Sukan sace mata da ba su da aure
Su auresu karhan suna fariya.
Rabbi ka kai ni Gwoza in gan su
Mutane na kirkin zaman lafiya.
Askira, Uba, Michika in je
Qasashe na Margi mutan lafiya.
’Yan kasuwan Bauchi caffa gare ku
Ku zauna da himmar zaman lafiya.
In shiga Maiha da Mubi in gan su
In ba su Waqar Zaman Lafiya.
Ku sai mun da nono idan na taho
Ku zan yin raha don zaman lafiya.
In zo ni Gombi in shiga Hong
Har ma da Song don zaman lafiya.
In na ga dama in je buga qwallo
Wasanmu golf ba ya shi ka jiya?
Ku bar ni in zarce wajen Yola dangi
Filani na Lamixo mai gaskiya.
Safiya ta bani abinci dafaffe
Da ’ya’yan itace tana dariya.
In kwan salati in je ga Inna
Da “Intel” da dukkan maso lafiya.
In kwana a gunta cikin so da qauna
Ta’ala ka bar mu ga baki xaya.
Nuhu Ribaxu aboki amini
Ina miqa caffa ga mai gaskiya.
Da sassafe in tashi in nufi Tilde
Ba ni da haufi cikin tafiya.
Da safe in je ni school in gane su
Teachers na ilmu cikin lafiya.
In isa Toro ga Katuka Sarki
Na samai da dangi cikin lafiya.
Ga yara da manya musamman ga mata
Ci gaba za mui ga baki xaya.
Ina ’yan uwana na Tilde ku zo
Kuna nan da shauqi kuna tambaya.
In shiga mota in kama hanya
Zuwa Ganye gun su mutan lafiya.
Wata ukku daidai babu Aliyu
Cuso na Nana maso lafiya.
In je ni in gana da danginmu Chamba
Da sarkinsu Gamwari mai gaskiya.
Yaro na Fatima har ma da Umma
Ga Luba can sun zaman lafiya.
In zo ni Numan, na sheqe ayata
Baqi na Benue zaman lafiya.
Na je can gidanmu in gaida Iro
Barhama Ghandinmu mai gaskiya.
Timawus Mathias in ganai har ya kaini
Gurin nasa gwarzon zaman lafiya.
In je kufayi in yi salati
Ziyara ga manya gidan gaskiya.
Sarkin ‘Bata in yi chaffa gare shi
In faxi gu nasa mai gaskiya.
In zo ni Zango in tadda ’ya’ya
Da mata da dangi suna lafiya.
Lamurde zan sayi kifi gasasshe
Na cinye a mota zaman lafiya.
In yi sujuda in gode Allah
Ta’ala ka zaunar da mu lafiya.
Ga Tula sun zo da tarba gare ni
Suna so in rera Zaman Lafiya.
Najeriyarmu gaba xai Afirika
Ka ba mu rabo da zaman lafiya.
Kaltungo, Villiri har ma da Kumo
Ku tashi ku miqe zaman lafiya.
Arewarmu Allah ka qare ta ilmu
Sana’a amana da son gaskiya.
Ku wo dandazon sallama don in gan ku
Ku ba ni aron kunnuwan lafiya.
Yaranmu Allah Ka shirye su Hadi
A hanya tsayayya su so gaskiya.
Ku kore su Shaixan ku zan yin zumunci
Ku zauna ku miqe cikin lafiya.
Manyanmu kau rabbi qare su tausai
Na yara, talakka da son mabiya.
Zan shiga Kumo domin in gan shi
Muhammadu Kumo kana lafiya?
Ka kore mugunta cikin zuciyarsu
Mayeta da hubbi ga baki xaya.
In ba su loto da baya tsawaita
Domin in zarce garin gaskiya.
Tammat fa waqe a nan zan aje ta
Ta cika baiti xari ba xaya.
Gombe ta Buba in sadu da dangi
Hausa da Fulve gaba ki daya.
Mai tambaya za ya ce wa ya yi ta
Zan ba ka amsa cikin gaskiya.
In shiga Makay in yi sayayya
In miqa katina don in biya.
Cene Aliyu na Tilde ya yi ta
Xan Usmanu mazajen jiya.
San Husein da Samaha sai na shige su
In qara sayayya, zaman lafiya.
A qarshe kirana ga Allah fiyayye
Ta’ala Ka tsarshe ni aikin riya.
Idan sun ka ce Ya Aliyu ka kwana
In ce musu a’a cikin dariya.
Ka karvi ibadunmu Rabbi Shakuru
Ka kare mu Sarkin zaman lafiya.
Zan kwana Bauchi da ikonSa Allah
Ta Yakubu garin zaman lafiya.
Iyaye jiqan su Ka sa su a Janna
Da Alkausara gun zaman lafiya.
In isa gu nasa Sarkin garinmu
In faxi domin zaman lafiya.
Ka qara salati bisa Annabinmu
Muhammadu manzon zaman lafiya.
In fita fadar ina taqama
Na zo gida kana ga lafiya.
In je gari in ga Tahir aboki
Muhamman Madaminmu mai gaskiya.
In nemi Habuna, Sadiqi na Mamman
Muhimmi gare ni wajen tafiya.
Ahmad Nadani ina zan gane ka
Ka ba ni shauqi cikin zuciya.
n Dokta Aliyu Tilde, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum